Kimiyya | 2. Tasirin Computer


Asalin Computer

Ƙidaya na da alfanu masu tarin yawa ga al’ummah. Misali gwamnati za ta so ta san yawan talakawanta ta hanyar ƙidaya don tasan yadda za ta rarraba masu albarkatun ƙasa cikin sauƙi. Ɗan kasuwa zai so ya ƙididdige ribar da ya samu. Mutum zai buƙaci ƙididdige kwanakin sati, wata da shekaru  don bayani da banbance lokacin da abubuwa suka faru ko zasu faru (don ƙididdigar lokaci). 


Sai dai, tun fil-azal, ƙidaya abubuwa masu yawa kalubale ne ga mutane. Wannan ne yasa mutane amfani da duwatsu, yatsun hannu, jadawalin kirga,alamar lambobi da lissafi don sauƙaƙe  ƙirga.


                                


                         


Lissafi wata dubarace ta  sauƙaƙe ƙirga. Misali idan mun san a makaranta mai aji biyu akwai dalibai 10-10 a kowane aji zamu zai fi sauƙi mu lissafa yawan daliban ta hanyar hada adadinsu 10+10 = 20 da ace mun tara su wuri daya mun maimaita ƙirga su. 


To saidai duk da cewa lissafi hanyce ta sauƙaƙe  ƙirga shima ƙalubale ne ga mutane. Wannan ne yasa ake amfani da na’urori kamar su abacus, kakuleta da computer don sauƙaƙe lissafi. 


Daga ƙarni na 17-19 anyi amfani kakuletoci masu motsi (mechanical calculators) kamar su arithmometer  wajen sauƙaƙe lissafi.Saidai basu da sauri (iya saurinsu iya saurin mai sarrafasu) kuma suna saurin lalacewa. 


                                    


A ƙarni na 19-20 Charles Babbage ya ƙirƙiro computer biyu masu aiki ta hanyar motsi (mechanical computer). Sune diffrence engine da analytical engine. Duk da cewa bai samu ya kammala ƙerasu ba. A wannan ƙarnin ne aka samu Ada Lovlace ta banbance tsakanin computer da kakuleta. Ita computer za a iya baya jerangiyar umarnin yin lissafi (programming) kuma ta ɗabbaƙa su daki-daki. Sannan computer zata iya yanke shawara idan wani abu ya faru. 


                                        
                                


A karni na 20 aka fara samun computer mai amfani da wutar lantarki sai dai computocin wuta na farko kamar colossus girman su ya kai girman ɗaki kuma suna fidda zafi mai yawa. Daga bisani aka samu cigaban kimiyya da ya bada damar samar da ƙananun computocin da muke amfani dasu a yau kamar laptop, wayar hannu da agogon zamani.

                                    


Mecece Computer 

Computer wata naaura ce da take sarrafa ɗaiɗaikun bayanai (data) don samun tattacen/dunƙulallen bayani (information) ta hanyar lissafi. Zaman bayani data ko information ya danganta da buƙata.

Alfanun Computer  

Computer na da alfanu masu dinbin yawa kamar a:

  • Kasuwanci

  • Tsaro 

  • Noma

  • Gudanar da gwamnati

  • Koyo da yada ilimi

  • Kiwon lafiya

  • Masana’antu 

  • Bincke

  • Kimiyya da fasaha

  • Sada zumunta

  • Sadarwa

  • d.s.s.


Amfanin Computer a Kasuwanci   


  • Dr Abubakar imam magana jari ce | bayani jari ne : A wannan zamani bayani na daga cikin jarin yan kasuwa. Masana harkan kasuwanci sun gano cewa shawarar da aka yanke ta hanyar tattara baynai tafi wacce aka yanke ta hanyar zato nesa ba kusa ba. Bayani kan kasuwanci zai nuna ma mutum in da kasuwancin ya dosa. ba kwastomomi abunda suke so.

  • Damarmaki: bayani zai iya nuna ma mutum ababen da kostomomi suke so game da kayan sayarwa, zai iya bayyana wata damar habaka kasuwanci

  • Matsaloli: zai nuna ma mutum abunda kostomomi basu so don ba kowane lokaci bane kostoma zai gaya ma abunda baiso.

  • A kan ajiye bayanan kasuwanci a littafi toh sai dai bayanin da aka aje a computer yafi saukin sarrafawa nesa ba kusa ba. 

  • Idan dankasuwa bai aje bayanan Kasuwanci shi ya kamata ya fara.



A Takaice

  • Muhimmancin da kalubalen kidaya

  • Hanyoyin saukake kidaya 

  • Amfani da na’urori don sauƙaƙe lissafi 

  • Kakuletoci da computoci masu motsi

  • Computoci masu aiki da lantarki

  • Computer na sarrafa bayanai ta hanyar lissafi 

  • Alfanu da illolin computer

Madogara 


Hotuna



No comments:

Post a Comment

Featured Posts

 

Popular Posts